Hebrews 5

1Kowanne babban firist, da yake an zabe shi ne daga cikin mutane, a kansa shi ya wakilci mutane ga al’amarin Allah, don ya mika sadakoki da kuma hadayu domin kawar da zunubai. 2Yana kuma iya tafiyar da jahilai da sangartattu a cikin salihanci, tun da shi ke rarrauna ne shi ta ko’ina. 3Saboda haka, wajibi ne ya mika hadayu, ba saboda kawar da zunuban jama’a kadai ba, har ma da na kansa.

4Ba wanda zai kai kansa wannan matsayi mai girma, sai dai Allah ya yi kiransa ga haka, kamar yadda aka kirayi Haruna. 5Haka kuma, Almasihu, ba shi ya daukaka kansa ya zama Babban firist ba, sai dai wannan ne ya sa shi, wanda ya ce da shi, “Kai Dana ne; Yau na zama Uba a gare ka.‘’

6Kamar dai yadda a wani wuri kuma ya ce, “Kai firist ne na har abada, bisa ga kwatancin Malkisadak.”

7Almasihu, a lokacin zamansa a duniya, ya yi addu‘o’i da roke-roke, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsannin mika kansa. 8Ko da yake shi Da ne, ya koyi biyayya ta wurin wuyar da ya sha.

9Har ya kai ga kammala, sai ya zama tushe madawwami, ceto ga dukkan wadanda suke masa biyayya. 10Gama Allah yana kiransa Babban firist, bisa ga kwatancin Malkisadak. 11Muna da abu da yawa da za mu fada a game da Yesu, amma zai yi wuyar bayani, da yake basirarku ta dushe.

12Ko da yake yanzu kam, ya kamata ku zama masu koyarwa, duk da haka, ashe, ba ku wuce wani ya sake koya muku jigajigan farko na Maganar Allah ba? har ya zamana sai an ba ku madara ba abinci mai tauri ba? 13To, duk wanda yake madara ce abincinsa, bai kware da maganar adalci ba, kamar jariri yake. Amma abinci mai tauri, ai, na manya ne, wato wadanda hankalinsu ya horu yau da kullum, don su rarrabe nagarta da mugunta.

14

Copyright information for HauULB